✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta sa a daure matashi a Kano kan zargin damfarar miliyan 30

An zarginsa da karbe kudaden mutane ne da sunan yin kasuwanci

Wata kotun majistare da ke zamanta Kano karkashin Mai Shari’a Mustapha Datti, ta ba da umarnin ajiye wani saurayi mai kimanin shekaru 27, a gidan gyaran hali kan zargin zamba cikin aminci da kuma cuta.

Matashin, mazaunin Unguwar Hotoro Danmarke dai ana zarginsa ne da aikata laifin wanda ya saba da sassa na 322 da 312 na kundin dokoki Jihar Kano.

Mai gabatar da kara, Asma’u A sani, ta shaida wa kotun cewa wanda ake zargin ya yaudari mutum 10 wajen karbar kudadensu da suka kai kimanin N30,060,500 yake kashe.

Lauyoyin masu kara, wadanda ke karkashin jagoranci Sulaiman Sale, sun bayyana sun ce wanda ake zargin ya karbi kudadensu da zummar yin kasuwancin shaddoji da atamfofi bisa alkawarin zai dawo da kudi da riba.

Bayan ya karbi kudaden, a cewar lauyoyin, sai ya saba alkawari ya koma juya su wajen amfanin kansa.

Bayan karanta masa kunshin tuhumar, Musa ya karyata zarge-zargen da ake masa.

Mai gabatar da kara ta roki kotu da ta dage zaman zuwa wata rana domin gabatar da shaidu.

Mai Shari’a Mustapha Datti ya ba da umarnin a ajiye wanda ake zargin a gyaran hali tare da dage zaman zuwa ranar 27 ga watan Satumban 2022.