✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tabbatar da nasarar Sanata Rufa’i Hanga

Kotun ta yi watsi da korafe-korafen da A.A Zaura ya gabatar.

Kotun Sauraron Korafe-Korafen Zabe ta tabbatar da nasarar Sanata Rufa’i Sani a matsayin dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kano ta Tsakiya.

Hakan dai na nufin Sanata Hanga na jam’iyyar NNPP ya yi galaba a kan Abdulsalam Abdulkarim Zaura, wanda shi ma ya yi takarar kujerar karkashin inuwar jam’iyyar APC a zaben da aka gudanar a watan Fabrairu.

Aminiya ta ruwaito cewa, tun bayan zaben ne dan takarar jam’iyyar APC wanda aka fi sani da A.A Zaura, ya kalubalanci nasarar da Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta tabbatar Rufa’i Hanga.

Tun a wancan lokacin ne A.A Zaura ta bakin lauyansa, Ishaka Dikko, ya nemi kotun sauraron korafe-korafen zabe da ta tabbatar da shi a matsayin wanda ya yi nasara.

A.A Zaura ya yi zargin cewa an tafka magudi a zaben Sanatan Kano ta Tsakiya wanda kuma ya ce cike yake da kura-kurai da sun ci karo da tanadin Dokar Zabe.

Sai dai a nasu martanin — Hukumar Zabe ta INEC da jam’iyyar NNPP tare da dan takararta da kuma tsohon Gwamnan Kano Ibrahim Shekarau — sun ce an gudanar da halastaccen zabe kamar yadda doka ta tanadar.

A yayin da suka yanke hukuncin a wannan Litinin din,alkalan kotun uku bisa jagorancin Mai Shari’a I.P Chima, sun ce A.A Zaura ya gaza gabatar da gamsassun hujjoji da ke nuna cewa an yi wa Dokar Zaben karan-tsaye a yayin zaben.

Kan haka ne ma Kotun ta yi watsi da korafin ta neman mai kara ya biya wanda ya yi kara N300,000 a matsayin diyya.