Kotu ta umarci Likitoci da su janye yajin aiki | Aminiya

Kotu ta umarci Likitoci da su janye yajin aiki

Likitoci
Likitoci
    Ishaq Isma’il Musa da Rejoice Iliya

Wata Kotun Masana’antu da ke zamanta a Abuja, ta umarci Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa a Najeriya da su janye yajin aikin da suke yi.

A hukuncin da yanke a ranar Litinin, Mai Shari’a John Tagrema ya umarci dukkan bangarorin da su jingine duk wani nau’i na bayyana fushi da ke tsakaninsu sannan su saurari hukuncin da za ta yanke a gaba.

Wannan na zuwa ne bayan da Gwamnatin Tarayya ta nemi kotun ta tilasta wa Likitocin da su janye yajin aikin.

Kungiyar Likitocin ta Nigerian Association of Resident Doctors NARD, ta ki amincewa da tayin da gwamnatin Tarayya ta yi mata da zummar ta janye yajin aikin da take yi.

Shugaban Kungiyar, Dokta Okhuaihesuyi Uyilawa ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron da suka yi da wakilan gwamnatin ranar Lahadi a Abuja.

Dokta Uyilawa ya ce sun ki amincewa da yarjejeniyar ce saboda akwai sakin layin da ba a fayyace musu ba duk da cewa Babbar Kungiyar Likitoci ta NMA ce ta kulla yarejejeniyar ce da gwamnati.

Ana iya tuna cewa, tun a ranar 1 ga watan Agusta ne Likitocin suka shiga yajin aikin na sai baba ta gani domin a biya musu bukatunsu.

A kan haka ne Ministan Kwadago, Dokta Chris Ngige ya mika batun hannun Kotun Da’ar Ma’aikata domin daukar mataki, inda wasu bayanai ke cewa gwamnati na son ta dakatar da biyan albashin likitocin da ke yajin aiki.