Kotu ta yanke wa barawon kaza hukuncin daurin shekara daya | Aminiya

Kotu ta yanke wa barawon kaza hukuncin daurin shekara daya

    Abubakar Muhammad Usman

Kotu ta yanke wa wani saurayi hukuncin daurin shekara daya da kuma biyan tarar N10,000 a kan satar kaza a garin Jos.

Alkalin babbar kotun yanki da ke zamanta a Kasuwar Nama a garin Jos da ke Jihar Filato, Mista Daniel Damulak, ya kuma umarci matashin da ya biya N5,000 ga wanda ya shigar da karar saboda rage masa asara

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan matashin mai shekara 17 ya amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.

Alkalin ya ce hukuncin zai zama izina da aya ga masu son shiga aikata laifuka.

Tun da farko, mai gabatar da kara, Mista Ibrahim Gokwat, ya bayyana wa kotun cewa an shigar da kara kan lamarin a ofishin ’yan sanda na yankin Laranto a ranar 8 ga watan Disamba 2021.

Ya ce matashin ya sace kazar ce ya yanka ta ya kuma soye ta, sannan suka yi wadakarta da abokansa.

Alkalin kotun ya ce laifin ya saba da sashe na 271 na kundin laifukan Jihar Filato.