✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Koli ta tabbatar da tube Aminu Babba Dan-Agundi

Kotun Koli ta Najeriya ta tabbatar da korar da marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya yi wa Aminu Babba Dan-Agundi a matsayin Sarkin Dawaki…

Kotun Koli ta Najeriya ta tabbatar da korar da marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya yi wa Aminu Babba Dan-Agundi a matsayin Sarkin Dawaki Maituta, Hakimin Gabasawa.

Da take karanta hukuncin, Mai Shari’a Mary Odili ta ce an yanke wannan hukuncin ne bisa la’akari da kudurin da alkalai biyar na kotun suka hadu a kai.

Hukuncin na zuwa ne shekaru shida bayan rasuwar Alhaji Ado Bayero.

A shekarar 2003 ne marigayin ya tube wa Aminu Babba Dan-Agundi rawaninsa bisa zargin rashin da’a.

An zarge shi da rashin biyayya ne dai bayan da marigayin ya gayyace shi fada, amma bai je ba.

Bayan tube shi ne ya kai karar Sarkin da Masarautar Kano wata babbar kotu, inda Alkali Sadi Mato ya yanke hukuncin a dawo da shi, a kuma biya shi dukkan hakkokinsa.

Daga nan ne Masarautar ta Kano ta daukaka kara, ita ma kotun daukaka karar ta tabbatar da hukuncin babbar kotun.

A karshe Masarautar Kano ta garzaya kotun koli, wadda ta tabbatar da matakin da marigayi Sarkin Kano Ado Bayero ya dauka na korar Aminu Babba Dan-Agundi.