✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kuɗin Tallafi: Abin da ma’aikatar jin-ƙai ta yi ba daidai ba ne — Akanta-Janar

Har shawara mu bai wa ma'aikatar kan matakan da za ta bi wajen biyan kuɗaɗen.

Babbar Akanta Janar ta Tarayya, Dakta Oluwatoyin Madein, ta ce ba ofishinta ne ke biyan kuɗin ayyuka ko wasu shirye-shirye da ma’aikatu da hukumomin gwamnatin suka aiwatar ba.

Ofishin babbar jami’ar shige da ficen kuɗin kasar na wannan furuci ne a matsayin martani kan fitar da wasu kuɗaɗe har N585,189,500.00 a matsayin tallafin masu ƙaramin ƙarfi na wasu jihohi da ma’aikatar jin kai ta ce ta yi bisa umarninta.

A bayan nan ne dai ministar harkokin jin kai da rage radadin talauci, Dokta Betta Edu, a cikin wata takarda mai dauke sa hannunta, ta ce ta fitar da kuɗaɗen ne bisa umarnin ofishin Akanta-Janar din ta asusun wani Oniyelu Bridget Mojisola.

Haka kuma, Rasheed Zubair, mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga ministan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, ya ce fitar da kuɗin da ma’aikatar ta yi yana kan turba ta ka’ida.

A cewar Zubair, an tura kuɗin cikin ga asusun Oniyelu Bridget Mojisola saboda kasancewarsa jami’in kula da shige da ficen kuɗin ayyukan biyan tallafi ga kungiyoyin masu ƙaramin ƙarfi.

Sai dai Dokta Madein ta yi martani kan wannan rahoton da tuni wasu kafofin yaɗa labarai suka watsa game da buƙatar ta ma’aikatar jin-ƙai da yaƙi da fatara, ta biyan kuɗin tallafi ga wasu masu ƙaramin ƙarfi a jihohin Ogun, Kuros Riba, Legas, da Akwa Ibom.

A cewar daraktan sadarwa na Ofishin Babbar Akanta-Janar, Bawa Mokwa, Dokta Madein ta ce fitar da kuɗin ayyuka ko wasu shirye-shirye da ma’aikatu da hukumomin gwamnati suka aiwatar a irin wannan yanayi ko kaɗan ba daidai ba ne.

A cewar Dakta Madien, ana ware wa kowace ma’aikata da hukuma kudaɗenta a asusun hukumarsu, kamar yadda yake ƙunshe cikin kasafin kuɗin, kuma kowace ma’aikata ita ce ke da alhakin gudanar da ayyukansu da biyan kuɗin ayyukan da ta aiwatar.

A cikin sanarwar da ofishin babbar akantan ya fitar, ta ce duk da ofishinta ya karɓi takardar buƙatar biyan kuɗaɗen daga ma’aikatar jin-ƙai da yaƙi da fatara ta ƙasar, amma ofishinta bai biya kuɗaɗen ba.

Ta ƙara da cewa ofishin nata ya shawarci ma’aikatar kan matakan da za ta bi wajen biyan kuɗaɗen kamar yadda dokar biyan kuɗaɗe ta tanadar.

Babbar Akantar ta kuma ce a irin wanna yanayi, ma’aikatun da abin ya shafa ne ke biyan kuɗaɗen zuwa asusun mutanen, ba tura maƙudan kuɗaɗe zuwa asusun wani mutum da sunan kuɗin gudanar ayyuka ba.

Ta ƙara da cewa a irin wannan biyan kuɗi ya kamata a tura kuɗin zuwa asusun mutanen da ake bai wa tallafin.

Daga ƙarshe sanarwar ta sake jaddada aniyar Dakta Madeine na yin aiki bisa doka ba tare da rufa-rufa ba wajen gudanar da kuɗaɗen gwamnati.

Ta kuma shawarci ma’aikatu da hukumomin gwamnati da koyaushe su tabbatar da sun bi doka da oda wajen gudanar da harkokin kuɗaɗe.