✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kuncin rayuwa ya sa matashi fadawa tekun Legas

Mutumin ya ajiye wata jakarsa ce sannan ya fada cikin ruwan

Kuncin rayuwa ya sa wani matashi mai shekara 28 ya hallaka kansa ta hanyar fadawa tekun Legas a yankin Elegushi da ke Jihar.

Rahotanni sun ce marigayin ya rika karakaina a gabar ruwan wajen misalin karfe 11:00 na daren Laraba, bakwai ga watan Yulin 2022.

Wata majiya daga jami’an ’yan sanda ta ce ba a gano dalilin zuwan mutumin gabar ruwan da wannan lokacin ba, inda aka gan shi ya ajiye wata jaka da yake rike da ita kafin daga bisani ya tsunduma cikin ruwan.

Sai dai bayanai sun nuna duk yunkurin da makwabtan wajen suka yi na ceto shi ya ci tura.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta Legas, SP Benjamin Hundeyin, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce gawar mutumin ta dago saman ruwa bayan kwana biyu da fadawarsa ciki.

Ya ce mutumin dan asalin yankin Ona Ara ne da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Ya ce bayan mutumin ya ajiye jakar da ya zo wajen da ita ce ya tsunduma cikin ruwan da ke Elegushi.

“A sakamakon haka, jami’an sashen kula da gabar ruwa na Rundunar ’Yan Sanda suka ziyarci wajen. An dauki hoton gawar mutumin kafin daga bisani a kai shi dakin ajiye gawarwaki,” inji Benjamin.