✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Miyetti Allah ta nemi majalisun dokoki su gyara dokar kafa Amotekun

Kungiyar Miyetti Allah (MACBAN) reshen Jihar Oyo ta ce bai kamata majalisun dokokin jihohin yamma su sanya hannu kan dokar kafa rundunar tsaro ta Amotekun…

Kungiyar Miyetti Allah (MACBAN) reshen Jihar Oyo ta ce bai kamata majalisun dokokin jihohin yamma su sanya hannu kan dokar kafa rundunar tsaro ta Amotekun ba tare da sanya ’ya’yanta a cikin runduna ba. Ta ce za ta ci gaba da fafutikar ganin an yi gyara kan doka musamman saboda yawan al’ummar Fulani a jihohin.

Shugaban kungiyar mai barin gado a Jihar Oyo Alhaji Yakubu Bello ne ya fadi haka a hira da Aminiya a Ibadan a inda ya ce “Fulani da ke zaune a Jihar Oyo su ne na 2 a yawan jama’a baya ga Yarbawa saboda haka bai kamata a tsame su daga muhimman abubuwan da za su kawo ci gaba a jihar da kasa baki daya ba. Muddin ana son ingancin tsaro a jihar to wajibi ne a yi adalci ba tare da nuna bambancin kabila ko addini a tsakanin al’umma ba.”

“Wadansu daga cikin mu Fulani, an haife su ne a nan Jihar Oyo fiye da shekara 70 kuma suke gudanar da kiwon dabbobinsu suke bayar da gudunmawarsu ga bunkasar tattalin arzikin jihar. Kuma muna zaune ne a dazukan kowane sako wanda dama ce gare mu ta fannin sanin kyawawa da miyagun abubuwan da rundunar Amotekun ba ta san da su ba da in ba a tsoma Fulani a cikin rundunar ba za a iya samun matsala,” inji shi.

Alhaji Yakubu Bello ya ce wadansu manyan sarakuna jihar kamar Alaafin na Oyo Oba Lamidi Adeyemi da Aseyin na Iseyin Oba Adekunle Abdulganiyu da Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin duk sun goyi bayan tsoma Fulani a rundunar Amotekun. Ya ce, “Yau shekara 20 ke nan da Kungiyar Miyetti Allah ta kirkiro ’yan sintiri da suke gudanar da ayyukan tsaro da jihohin Kudu maso Yamma suka yi maraba da su.’Yan sintiri da muka kafa a wannan sashi sun taka rawar ganikan tsaro da kama miyagun mutane musamman ’yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane da barayin shanu suna mika su ga ’yan sanda don hukunta su. To mene ne dalilin da zai sa a tsame mu daga wannan muhimmin abin ci gaban jama’a?”

Shi ma Sarkin Fulanin Jihar Oyo Alhaji Saliu Kadiri kira ya yi ga Gwamna Seyi Makinde da Majalisar Dokokin Jihar da su tsoma Fulani a cikin kungiyar Amotekun, inda ya ce gwamnatocin baya sun ga rawar da Fulani suka taka a kan tsaro.

A ranar Alhamis din makon jiya ne shugabannin majalisun dokokin jihohi 6 sun yi taro a Ibadan inda suka nuna rashin amincewa da tsoma ’ya’yan kungiyar Miyetti Allah a cikin kungiyar tsaro ta Amotekun.