✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyoyi za su maka Abba a kotu kan yunkurin nada kantomomi

Kungiyoyin na son dakatar da gwamnan Kano kan yunkurin nada kantomomi a jihar.

Kungiyar Hadakar Jam’iyyun Siyasa (IPAC) a Jihar Kano, ta yi barazanar maka gwamnatin jihar a kotu kan yunkurin nada kantomomi a Kananan Hukumomi 44 a jihar.

Wannan na zuwa ne, biyo bayan cikar wa’adin mulkin shugabannin kananan hukumomi a jihar.

IPAC ta bai wa gwamnatin wa’adin kwanaki bakwai don janye kudurinta na nada kantomomi a kan kujerun kananan hukumomin ko kuma ta maka ta a gaban kuliya.

Kungiyar ta yi zargin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fara yunkurin nada ma’aikatan da ya kai kananan hukumomin a kwanakin baya don zama kantomomi.

Kungiyar ta ce Abba ya nemi shugabannin kananan hukumomin jihar da su mika ragamar mulki ga shugabannin mulki na kananan hukumominsu.

Wakilin kungiyar a bangaren sharia, Barista Salisu Salisu Umar, ya ce yunkurin wani mataki ne na take hakkin al’umma.

Jam’iyyun siyasa 12 da suka hada da ADC da Accord da YPP da PRP da APGA da AAC da APC da Labour da APM da ADP suka sanya hannu kan hana gwamnan nada kantomomi.

A cewarsa “Kananan hukumomin su ne to turke na uku a Gwamnatin Najeriya. Sashe na 7 (1) na Kundin Tsarin Mulkin Kasa na shekarar 1999, ya hana nada kantomomi sai dai batun zabe.”

A cewar Barista Salisu, “Wannan abu da Gwamnatin Jihar Kano ke kokarin yi keta alfarmar dimokuradiyya ne wanda kuma ba za mu nade hannu muna kallon hakan ya faru ba.”