✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwalara ta kashe mutum 4 a Yobe

An fara feshin maganin kashe kwayoyin cututtuka a yankin nan take.

Mutum hudu sun riga mu gidan gaskiya yayin da wasu biyu ke kwance a gadon asibiti biyo bayan bullar cutar Kwalara a Karamar Hukumar Jakusko ta Jihar Yobe.

Babban Sakataren Hukumar Lafiya a Matakin Farko na Jihar Yobe, Dokta Babagana Kundi ne ya tabbatar da hakan a safiyar Alhamis.

A cewarsa, tuni aka tura tawagar gaggawa ta kwararru a yankin don shawo kan cutar.

“Yanayin dai tuni aka shawo kansa kuma na yi magana da Shugaban Tsare-Tsare na Cibiyar Lafiya inda na umurce shi da ya fara feshin maganin kashe kwayoyin cututtuka a yankin nan take” inji shi.

Shi kuwa Shugaban Karamar Hukumar Jakusko, Alhaji Abdullahi Hassan Gwayo, ya bukaci ma’aikatan lafiyar da su dauki matakan gaggawa don kare yaduwar cutar.

Gwayo, ya kuma shawarci al’ummar da ke yankin da su dabi’antu da tsaftar muhalli da sauran zamantewarsa kari a kan tabbatar da tsaftar abincinsu da na sha.