✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kwalara ta yi ajalin mutum 146 a Kebbi

NCDC ta ce mutane 816 suka mutu sakamakon harbuwa da cutar a Najeriya.

Mutum 146 aka tabbatar da mutuwar su a Jihar Kebbi sakamakon harbuwa da cutar kwalara wadda ke ci gaba da lakume rayukan jama’a a sassan Najeriya.

Hukumomin Jihar Kebbi sun ce mutane 146 aka tabbatar da mutuwar su na daga cikin mutane sama da 2,000 da aka iya tantancewa sun kamu da cutar.

Sakataren Asibitin Sir Yahaya da ke Birnin Kebbi, Aminu Bunza ya shaida wa manema labarai cewar mutane 2,038 suka harbu da cutar a fadin jihar tun bayan samun ta a Karamar Hukumar Sakaba.

Bunza ya ce bayan barkewar cutar a Dirin Daji dake Karamar Hukumar Sakaba yanzu haka cutar amai da gudawan ta yadu zuwa Kananan Hukumomi 20 dake Jihar.

Hukumar yaki da cututtuka a Najeriya NCDC a ranar Litinin ta ce mutane 816 suka mutu sakamakon harbuwa da cutar a jihohin Najeriya.

Daga cikin jihohin da cutar ta yi illa akwai Kano wadda ta yi asarar mutane 119 sai Katsina mai mutane 75, Zamfara na da mutane 30 sai kuma Sakkwato mai 23.