✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwamishinan muhalli na jihar Oyo ya rasu

Kwamishinan kula da muhalli na jihar Oyo kuma tsohon shugaban Majalisar Dokokin jihar, Honorabul Kehinde Ayoola ya rasu. Ayoola ya rasu ne da safiyar ranar…

Kwamishinan kula da muhalli na jihar Oyo kuma tsohon shugaban Majalisar Dokokin jihar, Honorabul Kehinde Ayoola ya rasu.

Ayoola ya rasu ne da safiyar ranar Alhamis a wani asibitin da ba a bayyana ba a birnin Ibadan bayan wata gajeriyar rashin lafiya.

Tsohon dan majalisar wanda ya wakilci mazabar Oyo ta Gabas da Oyo ta yamma a majalisar tarayya daga shekarar 1999 zuwa 2003 dan asalin kauyen Apaara ne da ke jihar.

Shi ne shugaban majalisar jihar daga watan Mayu zuwa Oktoba na shekarar 1999.

Ayoola ya kuma rike mukamin daraktan yakin neman zabe na Gwamnan jihar Seyi Makinde lokacin da ya yi takara a karkashin jam’iyyar SDP a zaben gwamna na shekarar 2015.