✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Kwanan nan karancin kaji da ƙwai zai kunno kai a Najeriya’

Kungiyar masu kaji da kwayaye ta kasa ce ta yi gargadin

Kungiyar Dillalan Kaji da Kwayaye ta Najeriya ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar a fuskanci karancin kaji da kwayaye sakamakon tsadar masara da waken soya da ake amfani da su wajen yin abincin kaji.

Kungiyar ta ce a sakamakon tsadar, yanzu sun koma dogaro da kayan abincin da ake shigowa da su daga ketare.

Kungiyar ta ce watakila ’yan Najeriya su fara sayen kaji da kwayaye masu tsada da ake shigowa da su masu tsada muddin gwamnati ta ki bayar da tallafin hatsi daga rumbunanta.

Da yake zantawa da manema labarai ranar Alhamis a Ikeja, Legas, shugaban kungiyar na kasa, Raymond Isiadinso, ya ce tsadar kwai da kaji dada kifi da sauran kayan gonar da ake amfani da su na da alaka ne da tsadar masara da waken soya.

Shugaban ya kuma ce masana’antar kaji na samar da ayyukan yi da kusan kaso 45 cikin 100, inda ya ce matsalar rashin ayyukan yi za ta karu idan bangaren ya fuskanci kalubale.

Ya ce kungiyar na bukatar a gaggauta hana shigo da irin waken soya da kuma masara domin abincin kaji.

Daga nan sai ya bukaci sabon Ministan Gona da Samar da Abinci, Alhaji Abubakar Kyari, da ya tashi tsaye wajen magance matsalolin a shirin samar da abinci.