Kwanan nan za a fara kashe kudaden Najeriya a China | Aminiya

Kwanan nan za a fara kashe kudaden Najeriya a China

    Hamisu Kabir Matazu da Sagir Kano Saleh

Bankunan kasar China za su fara karbar kudaden Najeriya nan gaba, kuma bankunan China za su shigo Najeriya domin fara aiki.

Jakandan kasar China a Najeriya, Cui Jianchun, ya sanar da cewa hakan zai taimaka wajen bunkasawa tare da saukaka gudanar da harkokin kasuwanci da zuba jari a tsakanin kasashen biyu.

Ya ce ofishinsa na aiki ka’in da na’in domin tabbatar da ganin bankunan Najeriya sun fara aiki a kasashen biyu, kuma “Manyan bankunan kasashen biyu na kokarin fara aiwatar da yarjejeniyar amfani da kudadensu a tsakaninsu; kuma za a fadada tsarin.

“Yanzu haka ina aiki domin ganin bankunan kasar sun shigo Najeriya sun fara aiki, bankunan Najeriya ma suna aiki a China,” inji shi.

Da yake bayani a wata tattaunawa da manema labaria a Abuja, hakan zai saukaka amfani da kudaden China da Najeriya a tsakaninsu wajen gudanar da kasuwanci da harkar masana’antu.

Mista Jianchun, ya yi fatan samun fahimtar juna tsakananin majalisun dokokin kasashen biyu a kan hakan.

Ya ce a watan Nuwamba mai kamawa ne za a gudanar ta taron ministocin kungiyar hadin kan kasashen Afirka da China karo na takwas a kasar Senegal.