✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwankwaso: Babu ruwana da takarar Wike a PDP

Ana zargin alakar Kwankwaso da Wike bayan ganin daliged din Kano sanye da jajayen huluna masu dauke da hoton Wike a taron PDP.

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya nesanta kansa da zaben fidda gwanin jam’iyyar PDP ko taimakon Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike a zaben.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Ibrahim Adamu ya fitar a yammacin ranar Asabar, inda ya ce ba shi da alaka da zaben na PDP.

“Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, jagora kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP ya lura da wani labari da aka yada a intanet, wanda ba komai ba ne face bata mishi suna.

“Rahoton wanda ke cike da karya, na cewa Sanata ya karbi Dala 15,000 daga hannun gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike don raba wa deligate din PDP.

“Idan ba a manta ba a ranar 29 ga watan Maris, 2022 Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fice daga PDP; Don haka babu tunani a ce mai neman takarar shugaban kasa zai bai wa jagoran jam’iyyar adawa kudi don neman daliget su zabe shi a jam’iyyarsa.

“Muna jan hankalin jama’a da su yi watsi da wannan labari. Sannan mun bai wa ‘Tabloid’ awa 48 da su fito su karyata labarin da suka wallafa sannan sun su bayar da hakuri wanda za a wallafa a manyan jaridu uku.

“Za mu dauki mataki a kan ire-iren wadannan kafafen yada labarai don zama izina ga wasu, wanda tuni lauyoyinmu suka fara shirin maka ‘Tabloid’ a kotu.

Tun da aka fara shirin gudanar da zaben fidda gwanin PDP an hangi wasu daga cikin daliget din Jihar Kano sanye da jajayen huluna mai dauke da hoton Wike.

Lamarin da ya sanya wasu da dama ke ganin Kwankwaso na da hannu wajen goyon bayan Wike a zaben fidda gwanin da ake gudanarwa a filin wasa na MKO Abiola da ke Abuja.