✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwastam ta kama kayan gwanjo da kwayoyin N20m a Kano

Hukumar Kwastam ta kama wasu kayan gwanjo da kwayoyi da aka shigo da su ta barauniyar hanya Jihar Kano. Shugaban Kwamitin Kar-ta-kwana na yaki da…

Hukumar Kwastam ta kama wasu kayan gwanjo da kwayoyi da aka shigo da su ta barauniyar hanya Jihar Kano.

Shugaban Kwamitin Kar-ta-kwana na yaki da Fasakaurin, O. A, Olurukoba ya ce kayan da kimarsu ta kai Naira miliyan 20 ne an kama su ne a ranar Talata.

Olurukoba ya ce galibim kayan an shigo da su ne daga kasashen da cutar COVID-19 ta yi wa katutu, wanda ya ce abun takaici ne shigo da irin kayayyakin a daidai lokacin da ake kokarin kayar COVID-19

Shugaban ya ce, hukumar ba za ta yi kasa a guiwa ba wurin yaki da masu safarar kowane irin kaya ta barauniyar hanya.

Olurukoba ya ci gaba da cewa, hukumar a shirye take ta bi ko’ina a fadin Jihar Kano domin kwace kayan da aka yi fasakwarinsu daga wani wuri zuwa jihar.

Ya ce yanzu sun daina kwace kaya kawai, sai an hada da tsare mai su a kuma gurfanar da shi a kotu kan laifin da ya aikata na karya doka.