✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Lebura ya yi wa abokiyar aikinsa fyade ya kashe ta

Wanda ake zargin ya jefar da gawar matar da ya kashe a cikin juji

Wani ma’aikcin gidan gona ya yi wa wata abokiyar aikinsa mai shekaru 55 fyade sannan ya kashe ta a wurin aiki.

Kotun majitare da ke Akure a Jihar Ondo, inda aka gurfanar da wanda ake zargin, ta ba da umarnin tsare shi.

Mai gabatar da kara Insfekta Anwana Josephine, ya shaida wa kotun cewa, bayan wanda ake zargin ya yi wa matar fyade, ya buga mata dutse a kai ta mutu, sannan ya jefar da gawar a cikin juji.

A cewar dan sandan, wanda ake zargin ya yi wannan aika-aika ne da misalin karfe 11 na dare a yannkin Oke-Odu da ke garin Akure.

Bayan sauraron karar, alkalin kotun, Mai Shari’a F A Aduroja, ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 27 ga watan Maris.