✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Lewandowski ya lashe kyautar gwarzon FIFA karo na biyu a jere

Wannan shi ne dai karo na biyu a jere da Lewandowski ya lashe kyautar.

A daren ranar Litinin ne Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA ta mika wa Robert Lewandowski kyautar gwarzon dan wasa na shekarar 2021 ajin maza.

Dan wasan kungiyar Bayern Munich da kasar Poland ya lashe kyautar FIFA ta gwarzon dan wasan shekara bangaren maza, la’akari da kwallayen da ya zura da kuma kofuna da ya lashe.

Wannan shi ne dai karo na biyu a jere da Lewandowski ya lashe kyautar bayan ya zazzaga kwallaye har guda 69 a raga.

Lewandowski mai shekaru 33 ya doke Mohamed Salah na Liverpool da kuma Lionel Messi na PSG wajen lashe wannan kyauta ta Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA.

Mika wa dan wasan kyautar ce ta sanya magoya bayan kwallon kafa ta dama suka rika kirayen-kirayen shi ya fi cancantar lashe kyautar Balon d’Or da aka bai wa Messi a watan Disambar da ya gabata.

Har yanzu dai Lewandowski ya gaza lashe kyautar Balon d’Or da wasu masu sharhi a fagen tamaula ke ganin ya cancanta ya samu a kakar wasanni guda biyu da suka shude.

Lewandowski ya goge tarihin da Gerd Muller ya kafa shekaru 49 da suka gabata na zama dan wasan da ya fi zura kwallo a raga a gasar Bundesliga a cikin kalandar wasanni a shekara guda.

Lewandowski ya yi nasarar zura kwallaye guda 43 cikin wasanni 34 da ya buga a gasar ta Bundesliga.

Dan wasan na Bayern Munich shi ne ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya na Fifa na 2020.

Dan wasan ya yi takara ne tare da dan kwallon tawagar Portugal, Cristiano Ronaldo a lokacin yana Juventus, da kuma tsohon dan wasan Barcelona, Lionel Messi na tawagar Argentina.

A wancan lokaci, Lewandowski ya ci kwallo 35 a wasa 47 a shekarar 2022 da hakan ya taimaka wa Bayern Munich ta lashe kofi uku a kakar da ta wuce.

Lewandowski shi ne dai dan wasan da ya zama kan gaba a cin kwallaye a Bundesliga da kofin kalubale da na Champions League a 2020.

Haka kuma, wannan shi ne karon farko da Lewandowski ya lashe kyautar da ya yi takara da dan kwallon Messi da Cristiano Ronaldo.