✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Likita ya naushi marar lafiya a yayin aikin tiyata

An zargi wani likita da naushin wata tsohuwa mai shekara 82 marar lafiya a lokacin da yake tsaka da yi mata tiyata a ido.

Duk inda marar lafiya yake a duniya tarairayarsa ake yi ballantana a asibiti ko uwa-uba dakin tiyata inda ake kokarin ceto ransa.

Sai dai ba haka ta kasance ba ga wani likita, wanda aka zarga da nannaushin wata marar lafiya a lokacin da yake tsaka da yi mata tiyata a ido.

Wannan lamari ya faru ne a kasar China ga wata tsohuwa mai shekara 82 lokacin da likitan ke yi mata aikin ido.

Likitan wanda ba a bayyana sunansa ba ya dunkule hannu ne ya naushe ta har sau uku cikin fushi.

Rahotanni sun ce tsohuwar ta rika motsa idonta ne da kanta saboda rashin tasirin allurar kashe laka a jiki domin yin tiyata, wanda hakan ya sa ta rika yin motsi likitan na tsaka da yi mata tiyata.

An ce likitan ya rika yi mata gargadi kafin a karshe ya naushe ta a fuska har su uku.

An ce tsohuwar ba ta fahimci abin da likitan ke fada ba, kasancewar ba ta jin harshen Mandarin wanda yake mata tsawa da shi, kuma hakan ya kai ga naushin ta, inda kyamarar CCTV ta dauki lamarin kuma wata likita ta yada wa duniya a dandalin sada zumunta, haka ya fusata dubban mutane a ciki da wajen kasar.

Bullar wannan bidiyo ya sa Hukumar Asibitin mai suna Aier Chaina amsa cewa lallai lamarin ya faru a daya daga cikin asibitocinsu a garin Guigang da ke Kudu maso yammacin kasar, kimanin mil 300 yamma da Tsibirin Hong Kong.

Sanarwar da asibitin ya fitar ta ce tuni ta dakatar shugaban asibitin da kuma likitan da ake zargi da naushin, wanda aka ce ya ji mata rauni a fuska.

Kuma a cewar danta hakan ya sa yanzu ba ta gani da ido daya, sai dai ba a sani ba ko sakamakon naushin ne ko kuma haka ta je asibitin.

“Bayan hakuri, sun ba mu Yuan 500 (kimanin Naira 775,00) na ban baki dangane da abin ya faru,” in ji dan wadda aka nausa.

Dokta Ai Fen wacce ta fitar da bidiyon, fitacciyar likita ce kuma daya daga cikin likitocin da suka kwarmata bullar cutar Kwarona a garin Wuhan, ta yi hakan ne bayan ta ci karo da bidiyon da asibitin da ma’aikatansa suka ja bakinsu suka yi shiru a kai, tun faruwar lamarin a watan Disamban shekarar 2019.