✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Litar fetur ta kai N400 a Taraba 

Masu ababan hawa a Jihar Taraba na fuskantar tsadar man fetur inda yanzu ake sayar da lita daya a kan Naira dari hudu.

Masu ababan hawa a Jihar Taraba na fuskantar tsadar man fetur inda yanzu ake sayar da lita daya a kan Naira dari hudu.

Matsalar ta fara ne a farkon makon jiya wanda inda daukacin gidajen man fetur a Jalingo suka daina sayar da mai illa kawai gidan mai na NNPC wanda ke wajen garin Jalingo.

Binciken Aminiya ya gano matsalar ta yi kamari inda tilas masu ababan hawa ke tafiya wasu garuruwa masu nisa daga garin Jalingo domin su sami man Fetur inda farashin ke da dan sauki.

Masu motocin haya da babura masu kafa uku da ake haya da su a garin Jalingo sun kara kudaden da suke karba a hannun fasunjoji.

Wani mai motar haya mai, Musa Adamu, ya zargi masu gidajen mai da boyewa suna kaiwa bayan gari su sayar wa ’yan bumburutu domin samun riba.

Amma wani daga daga cikin masu gidajen man da ya nemi a sakaya sunannsa ya ce zargin ba shi da tushe.

Ya ce ba sa samun mai a wajen manyan dilolin mai a Legas da Fatakwal.