✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Liverpool ta doke Atletico Madrid da ci 3 har gida

Liverpool ta je har gida ta doke Atletico Madrid ta ci 3 da 2.

Kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta sha kashi a hannun Liverpool har gida da ci 2-3 a gasar Zakarun Turai, a ranar Talata.

Antoine Griezmann ya zura kwallaye biyu, amma an ba shi jan kati, wanda hakan ya sa kungiyar ta yi rashin nasara na farko a rukunin B a gasar.

Tauraron Liverpool, Mohamed Salah ne ya zura kwallaye biyu, ciki har da bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Salah ne ya zura kwallo ta farko, sannan Naby Keita ya ci kwallo ta biyu, kafin daga bisani Atletico Madrid ta farke kwallo biyun baki daya.

Griezmaan ne ya fara farke wa Atletico Madrid kwallo ta farko a minti 20, sannan ya sake farke ta biyun, kafin tafiya hutu rabin lokaci.

Sai dai an ba wa Griezmaan katin sallama, minti bakwai bayan dawowa daga hutu, bayan takun da ya yi wa Roberto Firmino a ka.

Salah kuma ya zura wa Liverpool kwallo ta uku a raga a minti na 78 daga bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Yanzu Liverpool ce ke saman teburi a rukunin bayan lashe wasanni uku da ta yi, Atletico Madrid kuma a na biye mata baya a matsayin ta biyu a rukunin.