✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatan gwamnati maza za su fara hutun kwana 14 idan an yi musu haihuwa

Za a tsame ranakun hutu a lissafin kwanakin hutum ma'aikata.

Gwamnatin Tarayya ta amince a rika ba wa ma’aikatanta maza hutun kwana 14 idan aka yi musu haihuwa.

Sabon tsarin hutun da Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da shi a zamanta na ranar Laraba ya nuna daga yanzu za a rika lissafa hutun ma’aikata ne da ranakun aiki, sabanin ranakun kwanan wata da ake lissafa a baya.

Da take sanar da hakan, Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Folashade Yemi-Esan, ta ce maimakon tsarin da ake bi na jarabawar karin girma, yanzu za a koma auna ingancin aikin ma’aikata.

“Tun shekarar 2008 rabon da a sabunta wadannan tsare-tsaren aikin gwamnati; saboda haka abu ne da lokacin yin sa ya da dade da wucewa,” kuma an yi ne da gudunmawar masu ruwa da tsaki.