✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ma’aikatan wutar lantarki sun nemi a janye ƙarin kuɗin wuta

Sai dai gwamnatin tarayya ta ce ƙarin ba kowa da kowa zai shafa ba.

Ƙungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki, ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta sake nazari tare da janye ƙarin kuɗin wutar da ta yi a baya-bayan nan.

Wannan na cikin wata wasika da ƙungiyar ta aike wa ministan makamashi.

Ƙungiyar ta bayyana damuwarta da ƙarin, inda ta ce an samu tsadar kayayyakin abinci da kuma harkokin yau da kullum.

Wasiƙar da Sakatare Janar na ƙungiyar, Dominic Igwebike ya rattaba wa hannu, ta ce ƙarin kuɗin zai sanya wasu ‘yan Najeriya da ke da hannu da shuni su koma sayen kayayyakin da ake sarrafawa a ƙasashen waje.

Igwebike, ya kuma ce wannan zai iya sanya wasu kamfanoni sun rufe domin ba za su iya gogayya da wasu ba.

Sakataren ya kuma bayyana cewar ƙarin na iya jefa rayuwar ma’aikatan wutar cikin hatsari, sakamakon arangama da fusatattun mutanen da ake zuwa yanke wa wutar saboda gaza biyan kuɗin wuta.

Ma’aikatan sun zargi minista da yin gaban kansa wajen ƙarin kuɗin ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki a kan harkar ba.

Ƙungiyar ta bayyana cewar babu wata gajiya da talakan Najeriya zai ci game da ƙarin kuɗin da Gwamnatin Tarayya ta yi.

Idan za a iya tunawa Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC), ta amince da ƙarin kuɗin wutar lantarki ga abokan hulɗarta da ke ƙarƙashin tsarin Band A.

Sai dai ƙarin ya bar baya da ƙura, inda mutane da dama ke kokawa duba da yadda ake fuskantar tsadar rayuwa.