Mace ta maka Nuhu Ribadu da kasa a zaben fidda gwanin APC a Adamawa | Aminiya

Mace ta maka Nuhu Ribadu da kasa a zaben fidda gwanin APC a Adamawa

Sanata Aishatu Binani
Sanata Aishatu Binani
    Amina Abdullahi, Yola da Abubakar Muhammad Usman

Sanata mai wakiltar Adamawa ta Tsakiya, Aishatu Dahiru Ahmed Binani, ta maka tsohon Shugaban EFCC, Nuhu Ribadu, da kasa a zaben fidda gwani na Gwamna a jam’iyar APC a Jihar Adamawa.

Binani ta samu kuri’a 430, yayin da Nuhu Ribadu ya samu kuri’a 288.

Hakan dai na nufin Binanin ce za ta yi wa jam’iyyar ta APC takarar Gwamna a Jihar a zaben shekarar 2023 mai zuwa.

Muhammad Jibirilla Bindow, tsohon Gwamnan Jihar ya zo na uku da kuri’a 103 yayin da Abdulrazak Namdas ya zo a matsayi na hudu da kuri’a 94.

Kazalika Umar Mustapha Madawaki da Wafarniyi Theman sun zo a matsayi na biyar da na shida a zaben fidda gwanin da aka gudanar a ranar Alhamis a Jihar.