✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Magance matsalolin matasa ne babban muradina —Buhari

Buhari ya ce gwamnatinsa ta damu da matasan kasar nan.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce magance matsalolin da suka addabi matasa ne abin da gwamnatinsa ta sa gaba, domin cika alkawarinsa na samar da kyakkyawar makoma ga matasan Najeriya.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne lokacin da Babban Sakataren zauren samar da zaman lafiya na Abu Dhabi Forum, Sheikh Al-Mahfoudh Bin Bayyah, tare da takwaransa na Amurka, Fasto Bob Roberts, suka ziyarce shi ranar Talata a birnin Washington DC na kasar Amurka.

Buhari ya ce aikin da gidauniyar ke yi na inganta tattaunawa tsakanin addinai na da matukar muhimmanci ga duniya da ma Najeriya.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya fitar, ya ce akwai bukatar samar wa matasa yanayi mai kyau don guje musu fadawa cikin ayyukan masu tsattsauran ra’ayi, sannan ya bukaci kungiyar da ta ci gaba da kai dauki kan matasa don su ne manyan gobe.

“Ayyukan da kuke yi na da matukar muhimmanci musamman ga matasa.

“Wannan babban yunkuri ne da zai taimaka wa al’ummar da za su rayu nan gaba cikin aminci.

“A namu bangaren za mu ci gaba da magance matsalolinmu musamman wadanda suka shafi matasa.

“Muna da yawan jama’a kuma muna fuskantar kalubale masu tarin yawa, amma duk da haka muna kokari.

“A cikin shekara bakwai da rabi na yi iya bakin kokarina,” in ji Buhari.

Sakataren ya ce sun kai ziyarar ne don gayyata tare da karrama shugaba Buhari da gidauniyar ta shirya kan nasarorin da ya samu wajen inganta zaman lafiya da tsaro.

Ya kara da cewa karramawar wani sashe ne na aikin gidauniyar na yaki da tsattsauran ra’ayi da kuma samar da zaman lafiya a tsakanin addinai.