✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifiyar Dokta Bashir Aliyu Umar ta rasu

Marigayiyar dai ita ce mahaifiyar babban limamin masallacin Al-Furqan.

Allah Ya yi wa mahaifiyar fitaccen malamin addinin Islama a Jihar Kano, Dokta Bashir Aliyu Umar, wato Hajiya Khadija Harazumi, rasuwa.

Ta rasu da safiyar yau Talata a gidanta da ke Gwale Gudundi a cikin birnin Kano.

Daya daga cikin ’yan uwan malamin wanda ya tabbatar da rasuwar Hajiya Khadija ya ce za a gudanar ta sallar jana’izarta ne da misalin karfe 3:00 na yamma a Fadar Sarkin Kano da ke Kofar Kudu.

Marigayiyar dai daya ce daga cikin matan Dan Amar din Kano, Alhaji Aliyu Harazumi Umar.

Ta rasu ta bar ’ya’ya da jikoki da dama, cikinsu hard a Dokta Bashir, wanda kuma shi ne babban limamin masallacin Al-Furqan da ke Kano.