✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun hallaka mutane a kauyukan Binuwai

Akalla mutum tara sun rasu bayan mahara sun kai hari a kauyukan Jihar Binuwai.

Akalla mutum tara ne suka rasu bayan mahara sun kai farmaki a kauyukan Jihar Binuwai da tsakar dare.

Wasu da dama sun samu raunukan harbi sakamakon barin wutan da maharan suka yi ta yi tare da sarar mutane da adduna.

Mazauna kauyukan sun ce an kai harin ne da talatainin dare, kafin wayewar garin Juma’a a Kananan Hukumomin Guma da Gwer na Jihar.

Sai dai sun ce jami’an tsaro sun kawo musu dauki, wanda hakan ya tilasta wa maharan tserewa.

Sun ce jami’an tsaron sun kubutar da mutanen da suka samu raunuka, ciki har da wata mata ciki, da suka kai su asibiti ana kula da su.

Kakakin ’yan sandan Jihar Binuwai, Catherin Anene ba ta amsa kiran wayarmu ba ko rubutaccen sakon da muka aike mata.