✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe ’yan sanda 3 a Ebonyi

Maharan sun bude wa 'yan sandan wuta.

Wasu mahara sun hallaka jami’an ’yan sanda uku a daren ranar Litinin, a Jihar Ebonyi.

Wata majiya ta tabbatar da mutuwar ’yan sandan a gaban ofishinsu da ke kan hanyar Enugu zuwa Abakaliki da daddare.

Majiyar ta shaida cewar maharan sun bude wa ’yan sandan wuta ne bayan da suka tare hanyar bakin cajis ofis din da maharan ke kokarin wucewa ta wajen.

Majiyar ta ce “An dauki gawar jami’an zuwa dakin ajiye gawarwaki na asibitin Abakaliki, bayan likitoci sun tabbatar da mutuwarsu.”

Kakakin ’yan sandan Jihar ta Ebonyi, DSP Loveth Odah, ta tabbatar da faruwar lamarin.

Kazalika, ta ce ya zuwa yanzu babu wani cikakken bayani da za ta yi a kan lamarin.