✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kona akwatunan zabe 748 a ofishin INEC

Sun kona rumfunan zabe 240 na wucin gadi da kujeru da sauran kayan da ake amfani da su a rumufar zabe

Bata-gari sun kona akwatunan zabe 748 a wani hari da suka kai ofishin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) na Karamar Hukumar Igboeze ta Arewa a Jihar Enugu.

Kwamishinan INEC na Kasa kan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Barista Festus Okoye, ya ce maharan sun kuma banka wa ginin ofishin hukumar da ke karamar hukumar wuta.

Okoye ya ce, “Hukumar na aiki domin gano inda aka kwana kan batun ci gaba da rajistar masu zabe da kuma katunan zabe na dindinin da ke ajiye.”

Da yake jawabi a Abuja, Festus Okoye ya ce Kwamishinan Zaben INEC a Jihar Enugu, Emeka Ononamadu, ya sanar da hedikwatar hukumar cewa duk da jami’an kashe gobara da aka tura, wutar ta kuma lakume rumfunan zabe na wucin gadi 240 da kujeru da sauran kayan da ake amfani da su a rumufar zabe.

Jami’in ya ce aukuwar harin a yayin da ake tsaka da shirye-shiryen babban zaben 2023 abin damuwa ne matuka.

Ya ce a halin yanzu ’yan sanda na gudanar da bincike domin daukar matakin da ya dace.

“A ranar 23 ga watan Mayu 2021, ’yan bindiga sun kai hari a ofishinmu da ke a Karamar Hukumar Igboeze ta Kudu da ke makwabtaka da Igboeze ta Arewa.

“Gabaninsa an kai hari a ofishinmu na Karamar Hukumar Udenu ranar 13 ga watan Mayu, 2021 kafin a ranar 16 ga wata aka kai wa Babban Ofishin INEC na Jihar Engugu hari.

“Daidai gwargwado hukumar ta farfado bayan harin, ta ci gaba da gudanar da hakokinta ciki har da ci gaba da rajistar masu zabe da rabon katunan zabe da dindindin.

“Hukumar za ta ci gaba da aiki tare da jami’an tsaro da hukumomin kar-ta-kwana-kana domin kare kayan aikin INEC,” inji Okoye.