✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahara sun yi awon gaba da matan aure 3 a Zariya

’Yan bindigar sun farmaki yankin cikin daren ranar Alhamis.

An shiga zullumi a yankin Zango da ke Samaru a Karamar Hukumar Sabon Gari, Jihar Kaduna, bayan ’yan bindiga sun yi garkuwa da matan aure uku a daren Juma’a.

Yankin na Zango na makwabta da Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, a Jihar ta Kaduna.

Aminiya ta gano cewa ’yan bindigar da suka shiga yankin sun rika yin harbi kan mai uwa da wabi a cikin dare sannan suka yi garkuwa da wasu.

Kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai bayar da cikakken bayani game da mutanen da aka sace ba.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wasu ’yan bindiga sun shiga Makarantar Horar da Kananan Hafsoshin Soji (NDA) da ke yankin Afaka a Kaduna, suka kashe manyan hafsoshin soji biyu sannan suka yi awon gana da wani mai mukamin Manjo.