✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai kwacen waya da mota ta buge a Kano ya mutu

A safiyar nan ta Talata ce mai kwacen wayan ya ce ga garinku nan

Mai kwacen wayan nan da mota ta buge shi a Kano ya mutu, a cewar rundunar ’yan sandan jihar.

A safiyar nan ta Talata ce mai kwacen wayan ya ce ga garinku nan a inda aka kwantar da shi, “a Asibitin Murtala,” inji kakakin rundunar, Abdullahi Harun Kiyawa, ya sanar.

Aminiya ta ruwaito ranar Lahadi cewa mota ta mai kwacen wayan ne a lokacin yake kokarin tserewa bayan ya yi wa wata mata fashin wayarta.

Kakakin ’yan sandan jihar Kano, Haruna Abdullahi Kiyawa, ya ce mota ta kade shi ne a yayin da yake kokarin tsallaka titi bayan ya yi fashin.

A jiya, Kiyawa ya sanar cewa, “Bayan mun kai shi asibiti yana dan motsi, kashin bayansa ya karye (Spinal Code) kuma kansa ya fashe. Suna shawara su sa shi a “ICU”.”

Kwacen waya na daga cikin matsalolin tsaro da suka addabi jihar Kano, inda a wasu lokuta masu kwacen ka hallaka jama’a.

A sanadiyyar wannan matsala, gomman mutane a jihar sun rasa rayuwarsu a hannun masu kwace waya, wasa da dama kuma suka tsallake rijiya da baya da rauni ko asarar dukiya.

Lamarin ya dan yi sauki baya-bayan nan a sakamakon matakan da ’yan sanda da gwamnatin jihar suka dauka.
A wata hira a aka yi da gwamnan jihar, Abba Kabir yusuf ya sanar da afuwa da kuma shirin tallafin sana’a ga ’yan daba, wadanda da akasarinsu ke harkar kwacen waya.