✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Maigadi ya kashe ubangidansa a Gombe

Wani maigadi mai matsakaicin shekaru ya hallaka maigidansa a kauyen Malala da ke Karamar Hukumar Dukku a Jihar Gombe.

Wani maigadi mai matsakaicin shekaru ya hallaka maigidansa a kauyen Malala da ke Karamar Hukumar Dukku a Jihar Gombe.

Majiyar Aminiya ta ce maigadin, ya daba wa ogansa, Alhaji Abubakar Buba Galadima, mai shekar 50 wuka a talatainin daren Talata lokacin da ogan ya kai ziyarar ba-zata a gonar domin tabbatar da ko yana bakin aikinsa.

Kanin marigayin, Buhari Ahmed, ya shaida wa Aminiya cewa wan nasa ya noma wake ne inda ya dauki maigadin aikin lura masa da waken da aka yi roron su suke ajiye a gonar.

Ya ce, “Shi yayan namu ya bar gidansa ne da misalin karfe 12 na daren Talata a kan babur, da ya isa gonar sai ya saje kamar Da’u fataken dare, lamarin da ya sanya maigadin ya kama shi da kokawa.

“Amma wan namu ya rika shaida masa cewa ni ne fa –mai gonar, ko ba ka gane nib a ne?

“Da ya lura xan uwan namu ya fi karfinsa, sai maigadin ya zaro wuka ya caka masa a kirji; nan da nan ya ce ga garinku nan.

“Da ya fahimci abin da ya aikata, sai ya ruga gida domin sanar da mu cewa bisa kure ya daba wa ogansa wuka kuma ya mutu.

“Cikin hanzari muka tafi wajen inda muka tarar da shi jina-jina kwance kan wakensa,’’ inji shi.

Sai dai ya ce iyalan mamacin ba su da niyyar daukar matakin shari’a ko wani abu kan wanda ya yi kisan lura da makwabtan juna ne sannan ya yi ta da’war bisa kure ya kashe maigidan nasa.

Aminiya ta fahimci ’yan sanda a Dukku sun yi ram da maigadin, yayin da mai magana da yawun rundunar a Jihar Gombe, Mahid Muazu Abubakar ya shaida wa Aminiya cewa Kwamishinan ’yan sanda, CP Oqua Etim ya ba da umarnin a mayar da batun zuwa Sashen Binciken Miyagun Laifuka (SCID) na rundunar domin ci gaba da gudanar da bincike.