✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisa ta bukaci a hana Buhari fita waje neman magani

Ta ce hana Buhari neman magani a ketare zai sa a inganta Cibiyar Lafiya ta Fadar Gwamnati

Majalisar Dattawa ta bukaci a hana Shugaban Kasa Muhammadu Buhari fita kasashen ketare domin neman magani.

’Yan Kwamitin Raba Daidai da kuma Hulda Tsakanin Hukumomi na Majalisar ne suka bayyana haka a ranar Alhamis, a lokacin da Sakataren Fadar Shugaban Kasa, Tijjani Umar, ya bayyana a gabansu domin kare kasafin shekarar 2021.

Kwamitin ya ce hana Shugaba Buhari fita kasashen ketare neman magani zai sanya a inganta Cibiyar Kula da Lafiya ta Fadar Gwamnati da kuma tabbatar da ganin cibiyar ta fara aiki gadan-gadan a bana.

Ma’aikatar Fadar Shugaban Kasa ta gabatar wa majalisar kasafin Naira biliyan 19 da miliyan 700 wanda a ciki aka ware wa Cibiyar Lafiya ta Fadar Naira biliyan daya da miliyan 300.

Da yake tsokaci game da kasafin kudin, Shugaban Kwamitin, Sanata Danjuma La’ah, ya ce kwamitin zai amince da kudin da aka ware wa cibiyar amma bisa sharadin Shugaban Kasa da manyan mukarraban gwamnatinsa za su daina fita kasashen waje domin duba lafiyarsu.