Majalisar Dattijai a ranar Laraba ta bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya dakatar da shirinsa na takaita adadin tsabar kudaden da za a iya cira a kullum.
A makon da ya gabata ne dai babban bankin ya ce daga ranar tara ga watan Janairu mai zuwa za a takaita yawan kudaden da mutum zai cira zuwa N100,000 a kullum, sai kuma N500,000 ga kamfanoni.
Amma majalisar, bayan yin nazari kan rahoton kwamitinta na Harkokin Banki, ta bukaci CBN da ta jinkirta dokar saboda korafe-korafen jama’a.
Majalisar ta kuma bukaci kwamitin nata da ya sa ido yadda ya kamata a kan ayyukan bankin, sannan ya zo mata da rahoto.
Muna tafe da karin bayani…