Majalisar Dinkin Duniya ta nuna kaduwarta kan kisan fararen hula sama da 100 a Mali | Aminiya

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna kaduwarta kan kisan fararen hula sama da 100 a Mali

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres
    Bashir Isah

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna kaduwarta kan yadda aka kashe gomman mutane a makon da ya gabata yayin harin da wasu ’yan tawaye suka kai a kasar Mali.

An kau harin ne a makon jiya a tsakiya da kuma Arewacin kasar.

Majalisar ta bayyana kaduwarta ne cikin wata sanarwa da Babban Sakatarenta, António Guterres, ya fitar a ranar Laraba.

Rahotanni daga Kasar Mali sun ce, akalla fararen hula 100 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da ’yan-a-ware a kasar suka kai kan kauyuka da dama a yankin Bandiagara da ke kusa da Mopti.

Kazalika, sanarwar ta nuna damuwar Majalisar kan yadda aka raba dubban jama’a da mazauninsu a Ménaka da sauran wurare a tsakanin ’yan makonnin da suka gabata.

Guterres ya yi amfani da damar wajen mika ta’aziyyarsa ga ’yan uwan wadanda suka mutu da ma al’ummar Mali baki daya.

(NAN)