✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Kano na neman a kafa ’yan sandan jihohi

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bukaci a kafa ’yan sanda jihohi tare da rage wa Gwamnatin Tarayya karfi a jihohi da kananan hukumomi. Majalisar ta…

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bukaci a kafa ’yan sanda jihohi tare da rage wa Gwamnatin Tarayya karfi a jihohi da kananan hukumomi.

Majalisar ta kuma bukaci a yi wa kundin tsarin mulkin gyaran fuska domin bayar da damar kafa ’yan sandan jihohi wanda a cewarta zai taimaka wa jihohi magance matsalolin tsaro da suka yi musu dabaibayi.

Bukatun na Majalisar ginshikai ne na tsarin federaliyya wanda aka saurari ra’ayoyin jama’a a game da shi kan yi wa kundin tsarin mulki gyaran fuska.

’Yan Majalisar sun yi kiran ne a takardar bayan taron da Shugaban Majalisar, Hamisu Ibrahim Chidari ya rattaba wa hannu.