✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisar Kano ta dakatar da gina shaguna a jikin Asibitin Zana

Majalisar ta hana gina shagunan saboda saba wa doka

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta ba da umarnin dakatar da fara gina shaguna a jikin Asibitin Kula da Cututtuka Masu Yaduwa, wato Asibitin Zana da ke Jihar.
Umarnin ya biyo bayan wani kudurin gaggawa da dan majalisa mai wakiltar mazabar Fagge, Tukur Muhammad, ya gabatar a zaman majalisar na ranar Laraba.
Da yake zantawa da manema labarai bayan zaman majalisar, Muhammad, ya ce akwai zargin za a dauke babbar kofar shiga asibitin, wacce ke kan titin France Road a mayar da ita kan titin Whether Head, saboda gina shagunan.
Muhammad, wanda ya sauya sheka da ga PDP zuwa NNPP a baya-bayan nan, ya ce al’umma za su sha wahala wajen zuwa asibitin, idan aka gina shagunan.
Kazalika, ya shigar da korafin domin rashin dacewar gina shagunan, inda ya nuna gamsuwa da matakin majalisar na dakatar da ginin.
Ya kuma ce majalisar ta kafa wani kwamiti domin bincike da kuma hana irin wadannan gine-ginen a fadin Jihar.
A ’yan shekarun nan dai al’ummar Jihar na korafi kan yawan yanka filayen makarantu da asibitoci da masallltai bada ma makabartu don yin shaguna a kusan ko ina a birnin Kano.