✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Zamfara ta daina zama bayan garkuwa da mahaifin shugabanta

Majalisar ta dakatar da zama har sai an sako mutanen da aka yi garkuwa da su

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta dakatar da zamanta saboda garkuwa da mahaifin Shugabanta da ’yan bindiga suka yi mako uku da suka gabata.

Wata majiya mai tushe da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa Aminiya cewa tun bayan faruwar lamarin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta yanke shawarar dakatar da ayyukanta.

Wani babban ma’aikacin Majalisar ya ce faruwar lamarin ya girgiza ’yan majalisar, kuma “Akwai batutuwa da dama da ke bukatar kulawa, ciki har da jerin sunayen kwamishinonin da za a tantance, amma Majalisar ta dakatar da komai har sai an saki mahaifin Shugabanta cikin koshin lafiya.”

Majiyar ta ce yanzu kimanin mako biyu ke nan da aka ta karbi jerin sunayen kwamishinonin, amma ’yan majalisar sun riga sun yanke shawarar daina zama har sai an kammala maganar mutanen da ka yi garkuwa da su.

Kimanin mako uku da suka wuce ne ’yan bindiga suka kai hari yankin Magarya da ke Karamar Hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara, suka yi awon gaba da mahaifin Shugaban Majalisar.

’Yan bindigar sun kuma tafi da matar mahaifin Shugaban Majalisar da kawunsa da wasu karin mutum hudu lokacin da suka kai harin.

Mahaifin Shugaban Majalisar, Alhaji Muazu Abubakar, shi ne Mai Unguwar Sabon Garin Magarya da ke Gundumar Kanwa ta Karamar Hukumar ta Zurmi, wadda Shugaban Majalisar yake wakilta.

Majiyoyinmu sun ce an riga an fara tattaunawa da ’yan bindigar, amma suna ta ba da sharudda iri-iri yadda suka ga dama domin su sako mahaifin dattijon.

Aminiya ta gano cewa wani shugaban ’yan bindiga mai suna Halilu Kachalla ne ke taimaka wa hukumomi a jihar don ganin an sako mahaifin Shugaban Majalisar da sauran wadanda abin ya shafa.