Dubban ma’aikatan gwamnati, ciki har da ma’aikatan gidan waya da malaman jami’o’i da na kananan makarantu da sauransu, sun tsunduma yajin aiki a Birtaniya da zummar neman karin albashi.
Yajin aikin da aka soma ranar Alhamis ya jefa yanayin aiki a kasar cikin mawuyacin halin.
- Bakin haure 50,000 sun mutu a hanyar neman ingantacciyar rayuwa —IOM
- Gwamnati za ta lalata bindigogi 3,000 da ta kwato a hannun ’yan ta’adda
Ma’aikatan na neman a yi musu karin albashin ne don ba su damar iya yin rayuwa daidai da tsadar rayuwar da kasar ke fuskanta.
Makamashin girki da kayan abinci na daga cikin abubuwan da farashinsu ya yi tashin gwauron zabo, lamarin da ’yan kasar ke kokawa a kai.
Malamam jami’o’i kimanin 70,000 ne suka tsunduma yajin aiki a wannan Alhamis din a kasar, matakin da ya shafi karatun dalibai kimanin miliyan 2.5, inji rahotanni.