✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manchester City ta lashe Gasar Zakarun Turai karon farko a tarihi

A bana City ta yi wa duk sa’o’inta zarra a duk gasannin da ta haska.

Manchester City ta lashe Gasar Zakarun Turai karon farko a tarihi bayan shekara sama da 140 da kafuwar kungiyar.

City ta cimma wannan kadami ne bayan ta lallasa kungiyar Inter Milan da ci daya mai ban haushi a wasan karshe na babbar gasar tamaular ta Turai ajin kungiyoyi.

Dan wasan tsakiyar City na kasar Sifaniya, Rodri Hernandez ne ya jefa kwallo daya tilo a wasan wadda ta zama mafi muhimmanci a tarihin kungiyar.

Tun ba yanzu ba dai an yi hasashen cewa City ce za ta yi nasara a wasan la’akari da yadda ta yi wa sa’o’inta zarra duk gasanni da ta haska a kakar wasanni ta bana.

City ta taka rawar gani a wannan kaka wajen lashe manyan kofuna uku, da suka da Firimiyar Ingila da kofun kalubale FA sai kuma na zakarun Turai.

’Yan wasan na Pep Guardiola a yanzu sun taddo tarihin da Manchester United ta taba kafawa a shekarar 1999 na lashe dukkanin manyan kofuna 3 da suka fafata.

City ta dade tana fatan samun nasarar lashe gasar, inda a shekarar 2021 ta kai wasan karshe amma sai dai hakar ta bata cimma ruwa ba domin kashi ta sha a hannun Chelsea.

A shekarar da ta gabata ma dai, Manchester City ta yi yunkunrin kaiwa wasan karshe inda Madrid ta taka mata birki a matakin kusa da na karshe.