✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manchester United ta sha da kyar a wasanta na farko a Firimiyar Ingila

Sabon golan Manchester United, Andre Onana ya fidda ita kunya.

Manchester United ta sha da kyar wajen hada maki uku a wasanta na farko na Gasar Firimiyar Ingila da aka soma ranar Juma’a.

United dai ta tsallake rijiya da baya inda ta samu nasarar yi wa Wolverhampton ci daya mai ban haushi a karawar da suka yi a daren jiya na Litinin.

Raphael Varane ne ya zura kwallo a minti na 75 da fara wasa a lokacin da Manchester United ta samu nasara a kan Wolves a filin wasa na Old Trafford.

Tawagar Erik ten Hag dai ba su kai wasu hare-haren kirki ba, har sai da Bruno Fernandes ya samu Aaron Wan-Bissaka da kyakkyawar kwallo a bangaren ragar Wolves.

Dan wasan baya na dama a matse ya jefo kwallon ta bangaren ragar Wolves, inda Varane ya yi amfani da tsayinsa ya ketare Nelson Semedo.

Wannan lamari ya yi wa Wolves ciwo ainun, ganin cewa kocinta, Gary O’Neil yana neman nasararsa ta farko a wannan kungiya da ya karbi aikin horar da ita.

O’Neil ya samu katin gargadi a lokacin da ya yi ta hargowa yana neman alkalin wasa ya ba tawagarsa bugun daga kai sai mai tsaron raga a kusan karshen wasa.

Haka kuma, mai tsaron ragar United Andre Onana ya kaucewa hukunci a karin lokacin, bayan ya yi karo da Sasa Kalajdzic lokacin da ya yi yunkurin kama kwallo amma ya kuskure ya doke dan wasan na Wolves.

Duk da haka, kwallayen da Onana ya tare a cikin wasan na da matukar muhimmanci, kuma tsohon dan wasan Ajax da Inter Milan din ya samu karbuwa wurin magoya bayan United da su ka kalli wasan a filin Old Trafford.