Manzon Allah: Haske mai kore duhu (40) | Aminiya

Manzon Allah: Haske mai kore duhu (40)

 Masallacin Annabi (SAW) da ke Madina
Masallacin Annabi (SAW) da ke Madina
    Ustaz Aliyu Muhammad Sa’id Gamawa

Manzon Allah: Haske mai kore duhu (40)

Yan shekaru wannan magana ta tabbata domin lokacin Halifanci Usman (RA) yana Sham amma yawan yin zazzafan wa’azinsa ga masu son duniya ya sa aka mayar da shi Madina. Usman (RA) ya nemi ya zauna tare da shi, ya vi ya ce ba ya son abin duniya sai dai ya nemi izini ya koma can wani wuri gaba da Madina ‘Rabaza,’ ya zauna shi kadai sai matarsa da bawansa ba a dade ba ya rasu. Yana rasuwa sai ga su Abdullahi dan Mas’ud tare da wadansu sahabbai daga Iravi, bawan ya sanar da su Abu Zar ne, a nan Ibn Mas’ud ya yi kuka kuma ya jagoranci yi masa Sallah suka rufre shi a can.

Sannan akwai kuma munafukan da aka tafi da su Tabuka, amma su vovarinsu su bavanta ran Manzon Allah (SAW) don haka da aka rasa ruwan sha har aka yanka rakumi shi ne suke cewa da shi Manzon Allah (SAW) ne da ya yi addu’a an sauko da ruwa kamar yada Annabi Musa (AS) ya yi. Da labarin ya kai masa sai Abubakar (RA) ya ce ka yi mana (addu’a) ya Manzon Allah! Lallai Allah zai karba maka, daga nan ya daga hannayensa ya yi addu’a nan da nan hadari ya hadu take aka zubo ruwa kamar da bakin vwarya kuma bayan an gama da suka fita wurin nan kadai ne aka yi ruwan daidai inda suke.

Bayan wannan taguwarsa Vaswa ta bata suna hutawa a wani wuri sai ana nemanta nan ma munafukai suka samu abin fadi cewa wanda ake bai wa labari daga sama amma a ce bai san inda taguwarsa ta shige ba. Da ya ji yake cewa ai sai Allah Ya ba ni labari ni ma nake sani. Sannan ya ce Allah Ya gaya masa tana tsakanin tsaunin can kanta ya sarvafe a tsanin itaciya. Sahabbai na zuwa suka same ta a wurin kanta ya sarvafe.

Bayan tafiya ta nisa sun sauka a vasar Samudawa (Hijr) da suka kawo inda Samudawa suka zauna, sai Manzon Allah (SAW) ya umarce su kada su bi ta cikin gidajen wadanda suka zalunci kawunansu kada abin da ya same su ya same ku. Ruwan da suka jawo a rijiyar ya hana su sha ko alwala wanda aka kwaba garin d za a yi gurasa da shi ya ce su bai wa dabbobi. Sannan ya dukar da kai ya yi tafiya sauri-sauri har suka fice kwarin.

Bayan sun sauka a Tabuka wanda shi ne wuri na goma sha tara da aka sauka a tafiyar. Abu Khaisama shi ma ya riske su ya kasance mumini mai gaskiya kafin a fito wannan tafiyar ba a fito tare da shi ba, kuma ba da wani uziri ba, da har ya zauna yana hutawa a inuwa ga matansa sun tanadar masa abinci da ruwa mai sanyi kawai ya ce Manzon Allah (SAW) yana rana ni kuma a inuwa da kyawawan mata? Ya rantse ba zai shiga wurin ko daya (daga cikin matan) ba har sai ya hadu da Annabi (SAW). Shi ne ya taho ya same su a Tabuka. A nan Manzon Allah (SAW) ya yi musu wa’azi mai cike da fa’ida, kuma bayan ya gama Tahajjud ya sanar da su wasu abubuwa biyar da Allah Ya ba shi wadannda bai taba bai wa wani Annabi dukka ba kafin shi. Cikinsu har da sanya vasa ta zama masallaci da tsoron nisan wata daya da maviya suke ji a tsakakninsu da shi.

Zaman da aka yi a Tabuka

Manzon Allah (SAW) ya shawarci sahabbai su wuce ne ko su tsaya, a nan aka yanke shawarar tsayawa. Sai ya aiki Khalid dan Walid ya je Daumatu Jandal ya taho da shugabansu Ukhaidir dan Abdulmalik tare da mahaya dari hudu. Khalid ya jinjina ta yaya zai gane shi a gari mai yawa. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce za ka gan shi yana farautar saniya da Khalid ya je garin ya gan shi yana vovarin kama wata saniya da take tunkurar vofa, nan ya kama shi ya kawo shi wurin Manzon Allah (SAW). An kira su (zuwa ga) Musulunci sai dai ba su karba ba, amma an yi sulhu kan za su riva ba da Jizya.

Rumawa sun san da saukar Musulmi a Tabuka amma ba su yi kasadar fitowa (don) karawa da su ba, sai ma suka warwatsu suka nausa cikin garuruwansu. Manzon Allah (SAW) ya zauna a cikinta (Tabuka) tsawon kwana ashirin yana tsoratar da maviya kuma yana karbar masu shigowa Musulunci daga wurare daban-daban, wadansu kuma sulhu ya kawo. Haviva Yuhanna dan Ru’ubah ya zo Shugaban Ailah da wadanda ya zo da su mutanen Jarba’a da Azruh da Maina’a suka yi sulhu a kan za su riva ba da Jizya. Ya bayar a rubuce ga Yuhanna samun aminci da mutanen Ailah da alvawarin aminci ga hanyar jiragen ruwansu da abubuwan hawansu na tudu da ’yancin tashi da sauka a wuri. Su ma mutanen Jarba’a da Azruh an ba su aminci kowanensu zai bayar da Dinari dari duk watan Rajab. Maina’a kuma za a karbi rabin ’ya’yan itacensu duk shekara.

Bayan cikar kwana ashirin ba alamun wanda ya shirya yavi sai suka shirya baro Tabuka sai dai Musulmi sun samu katsewar abinci sai suka nemi izini daga Annabi (SAW) su yanka ravumansu har an yanka daya Umar (RA) ya hana su ya samu Annabi (SAW) ya ce, idan suka ci gaba da haka za a rasa abin komawa ko zai rova musu Allah abincin da suke da shi ya yi albarka? Manzon Allah (SAW) ya yarda sai ya yi alwala ya yi Sallah ya kuma rovi Allah sannan ya shimfida vyalle aka zuba duk abincin da suke da shi wanda bai wuce sa’i uku ba, ya umarci kowa ya zo ya debi yadda zai iya ci. Haka suka yi ta diba suna ci har kowa ya voshi amma kamar ba a taba shi ba. Sannan suka nufi Madina, sun yi kwana goma sha biyar a hanya, idan aka hada da na tahowarsu da zamansu a Tabuka sun kwashe kwana hamsin rabonsu da Madina.

Ana cikin tafiyar ce da aka zo Avaba sai rundunar ta bi ta kwarin shi kuma Manzon Allah (SAW) ya bi ta Avabar ba wanda yake tare da shi a lokacin sai Ammar (RA) yana rive da akalar dabbar Manzon Allah (SAW) sai Huzaifa kuma yana bayanta yana kora ta. Sai wadansu mutum 12 suka biyo bayansu daga cikin munafukai da nufin kashe Manzon Allah (SAW) har sun kusanto shi sai Manzon Allah (SAW) ya ce da Huzaifa ya je ya doddoki fuskokin abubuwan hawansu da abin da yake hannunsa. Da ya je ya aikata haka sai Allah Ya jefa musu tsoro a zukatansu suka juya da gudu suka shige cikin ayari da ma an yi masa wahayi aka sanar da shi cewa da dare za a zo da nufin hallaka shi.

 

Za mu ci gaba insha Allah.

 Za a iya samun Ustaz Aliyu Muhammad Sa’id Gamawa ta +2348023893141 ko imel:aliyugamawa@gmail.com