Marasa addini na bai wa ’yan Kenya tallafin asibiti don raba su da addininsu | Aminiya

Marasa addini na bai wa ’yan Kenya tallafin asibiti don raba su da addininsu

Taswirar kasar Kenya
Taswirar kasar Kenya
    Muhammad Aminu Ahmad

Wadansu wadanda ba sa bin addini a
Kenya na taimaka wa mutane da kudin jinya da daukar nauyin jana’izar ’yan uwansu da zimmar raba su da addinansu.

Kungiyar mai suna Atheists In Kenya Society (AIK) ta fuskanci koma-baya lokacin da sakatarenta na kasa ya bar mukaminsa kuma ya koma addinin Kirista.

Yanzu jungiyar tana rokon duk wanda “ba ya bin addini, wanda bai damu da addini ba, wanda bai yarda da samuwar Allah ba” da ya je shafinta ya biya wasu kudi don yin rajista don ya samu tallafin asibiti.

Fiye da kashi 97 cikin 100 na ’yan Kenya na bin addini, a cewar binciken cibiyar Pew Research.