✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masarautar Bauchi ta tube rawanin sarakai 6

Masarautar ta dakatar da Haikimin Galambi daga yin nadin sarauta na tsawon shekara guda

Masarautar Bauchi ta tube rawanin wasu sarakai shida a yankin Hakimin Galambi.

Jami’in yada labaran masarautar, Babangifa Hassan Jahun ya ce majalisar masarautar ta soke nadin sarakan da abin ya shafa ne saboda Hakimin Galambi bai bi ka’ida ba wajen nada su.

Ya kara da cewa masarautar ta dakatar da Haikimin ne Hakimin Galambi, Alhaji Shehu Adamu Jumba daga yin nadin sarauta na tsawon shekara guda, daga ranar 7 ga watan Nuwamba, sannan wajibi ne ya bi ka’ida nan gaba wajen yin nadin sarauta.

A kwanakin baya ne Hakimin Galambi wanda shi ne Danlawal na Bauchi, ya yi wa wasu mutanen shida nadin sarautar Galadaman Danlawal, Wakilin Dokan Danlawal d kuma Majidadin Danlawal.

Sauran su ne Wakilin Gonan Danlawal, Sarkin Dajin Danlawal da kuma Hardon Danlawal.