’Yan bindigar da suka yi garkuwa da dan Majalisar Dokokin Jihar Taraba sun nemi a biya su kudin fansa Naira miliyan 150.
Masu garkuwar sun tuntubi iyalan Bashir Muhammad mai wakiltar Mazabar Nguroje a yankin Sardauna wanda suka sace a gidansa a Jalingo a daren Alhamis.
- Maharan da suka je garkuwa da magidanci sun dauke matarsa
- ’Yan majalisa ba su da hurumin gayyatar Buhari —Malami
Majiyarmu ta ce ana kan tattauanwa tsakanin dangin Bashir Muhammed da masu garkuwa da mutanen.
Majiyar ta ce ’yan bindigar sun dage cewa dole sai an ba su kudin da suka nema kafin su sako shi.
Bashir Muhammed wanda ke cikin firgici ya roki shugabannin majalisar dokoki kuma gwamnatin jihar ta Taraba da su taimaka su biya bukatun masu garkuwar domin ceto rayuwarsa.
Tuni dai ’yan majalisar dokokin jihar, a cewar wata majiya ta gana da Gwamna Darius Ishaku kan batun.