✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu garkuwa na neman N20m kan dan tsohon Sakataren Kungiyar Likitoci

’Yan bindiga na neman kudin fansa Naira miliyan 20 kafin su sako dan tsohon Sakataren Kasa na Kungiyar Likitoci ta Najeriya (NMN), Dokta Adewunmi Alayaki,…

’Yan bindiga na neman kudin fansa Naira miliyan 20 kafin su sako dan tsohon Sakataren Kasa na Kungiyar Likitoci ta Najeriya (NMN), Dokta Adewunmi Alayaki, da suka yi garkwua da shi a Jihar Ogun.

Wakilinmu ya gano cewa ’yan bindiga sun kutsa gonar Dokta Adewunmi da ke Isaga-Orile a Karamar Hukumar Abeokuta ta Arewa suka yi awon gaba da dan nasa mai suna Adedamola zuwa inda ba a sani ba.

Kakakin ’yan sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar wa manema labarai cewa jami’an rundunar na bin sawun ’yan bindigar domin kubatar da Adedamola “wanda shi ne manajan daya daga cikin gonakin mahaifinsa.”

“Muna bibiyar lamarin kuma jami’an na bin sahun bata-garin,” inji shi.