✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Masu zanga-zangar neman tallafi a Jos sun daba a kas’

Gwamnatin Filato ta ce zanga-zangar da wasu mata suka yi a Jos, babban birnin jihar, ranar Asabar ba ta da wani amfani. Kwamishinan Yada Labarai…

Gwamnatin Filato ta ce zanga-zangar da wasu mata suka yi a Jos, babban birnin jihar, ranar Asabar ba ta da wani amfani.

Kwamishinan Yada Labarai Dan Manjang ne ya fadi haka, sannan ya ce da matan sun yi zaman su a gida, idan akwai sunayensu a cikin wadanda za a baiwa agajin suna zaune za a kirawo su.

Kwamishinan, a wata zantawa da ya yi da wakilinmu, ya ce wasu marasa kishin kasa ne suka yaudari matan suka ce su zo wai za a ba su tallafin N30,000 ko waccensu.

COVID-19: ‘Plateau na bincike kan kwarmata sakamakon gwaji’

Coronavirus: ‘Dalilin dakatar da komai a Filato’

Ya ce sam gwamnati ba ta ce matan su taru don a ba su N30,000 ko tallafin kayan jinkai ba.

“Wannan tallafin kayayyakin jinkai da gwamnatin Filato ta ce za ta bayar an fara bayar da shi jiya a garin Bukur da ke karamar hukumar Jos ta Kudu.

“Kuma an tsara yadda za a raba wadannan kayayyaki tun daga matakin jiha zuwa kananan hukumomi da gundumomi, tare da kafa kwamitocin da za su gudanar da wannan aiki”, inji Mista Manjang.

A jiya Asabar ne dai wasu daruruwan mata dauke da ganye suka yi zanga-zanga suna nuna takaici da rashin samun kayayyakin tallafin jin kai da gwamnatin jihar ta ce za ta raba wa al’umma don rage musu radadin dokar hana fita da aka kafa.

Matan sun shaida wa ‘yan jarida cewa suna zanga-zangar ne saboda gwamnati ba ta ba su tallafin da ta yi alkawarin za ta ba su ba.

Jihar ta Filato dai ta bi sahun jihohin Najeriya da dama da suka ayyana dokar hana fita sam-sam da nufin hana cutar coronavirus shiga yankunansu.