✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata fiye da 30 ke takara a zaben kananan hukumomin Abuja

Mata fiye da 30 ne suka tsaya takarar mukamai daban-daban a zaben kananan hukumoin Abuja

Asabar din nan, 12 ga watan Fabrairu, ake gudanar da zaben kananan hukumomi a Yankin Birnin Tarayya.

Wani abu da watakila ya bambanta wannan zaben da ire-irensa da ake yi a wasu sassan Najeriya shi ne yawan matan da suka tsaya takara.

Binciken Aminiya ya gano cewa a tsakanin masu fata a rantsar da su a matsayin shugabar karamar hukuma da masu sa rai da mukamin mataimakiyar shugaban karamar hukuma, akwai mata 11.

Matan da ke neman darewa kujerar shugaba a kananan hukumomin dais u uku ne, yayain da mata takwas suke neman kujerar mataimakiya.

Kallabi tsakanin rawuna?

Bugu da kari, kamar yadda shafin intanet na Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ya nuna, mata kusan 30 ne ke neman hawa kujerun kansilolin kananan hukumomi shida na yankin.

Duk da cewa idan dubi yawan ‘yan takara mai yiwuwa wannan adadi na mata bai kai abin da ake ta kiraye-kiraye a matakai daban-daban a bai wa mata ba, wannan ma ci gaba ne bisa la’akari da cewa a wasu wuraren yawan matan da ke tsayawa bai taka kara ya karya ba. A wasu wuraren ma babu sam.

Jam’iyyu 14 ne suka tsayar da ’yan takara a matakai daban-daban na zaben kananan hukumomin na Abuja.

Ga dai jerin sunayen matan da suka yi kukan kura suka shiga takarar shugabancin da kananan hukumomin da suke takara:

Karamar Hukumar Kwaryar Birnin Abuja

Princess Nneka E Nebo – Shekarunta 41 a duniya, kuma tana neman mukamin Mataimakiyar Shugaban Karamar Hukuma ne a karkashin jam’iyyar PDP;

Tor Manager Mdoo Naomi – ’Yar takara mai shekara 33 da ke fata ta zama Mataimakiyar Shugaban Karamar Hukuma;

Eke Patience Ndidi – Ita ma tana da burin zama Mataimakiyar Shugaban Karamar Hukuma;

Queen Oyibo Okpe – Mai neman zama Mataimakiyar Shugaban Karamar Hukuma. Shekarunta 33.

Aminat Mohammed – ‘Yar  takara mai shekaru 33 da haihuwa, ita ma za a fafata da ita ne wajen neman mukamin Mataimakiyar Shugaban Karamar Hukuma;

Samuel Horsefall Chikaba Mina – Shekarunta na haihuwa 35, kuma tana neman zama Shugabar Karamar Hukuma ne.

Karamar Hukumar Bwari

Mary Fajenyo – ’Yar takara mai shekaru 34 da ke fatan zama Mataimakiyar Shugaban Karamar Hukuma;

Ibitokun Patience Bunmi – Burinta shi ne zama Shugabar Karamar Hukuma. Shekarunta 36;

Ogah Patricia Odoh – Shekarunta 33, kuma ita ma tana neman mukamin Shugabar Karamar Hukuma ne.

Karamar Hukumar Gwagwalada

Musa Justina – ’Yar takara mai shekaru 33, tana da burin zaman Mataimakiyar Shugaban Karamar Hukuma;

Karamar Hukumar Kwali

Magdalene Danjuma – Ita ta fi kowa kuruciya a cikin matan da ke neman zama Shugabar Karamar Hukuma ko Mataimakiya domin kuwa shekarunta 30. Tana neman mukamin Mataimakiyar Shugaban Karamar Hukuma ne.