✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata gajiyayyu 18,000 za su amfana da tallafin rage radadin COVID-19

Ma’aikatar Harkokin Mata da hadin gwiwar Hukumar Yaki da Cuta Mai Karya Garkuwar Jiki ta Kasa (NACA) da sauran kungiyoyin ba da tallafi na duniya…

Ma’aikatar Harkokin Mata da hadin gwiwar Hukumar Yaki da Cuta Mai Karya Garkuwar Jiki ta Kasa (NACA) da sauran kungiyoyin ba da tallafi na duniya sun kaddamar da wani tallafi don taimakawa mata gajiyayyu su rage radadin annobar COVID-19.

Sauran masu tallafin sun hada da Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai kuma akalla mata 18,000 ne ake sa ran za su ci gajiyarsa.

A wata sanarwa da NACA ta fitar ranar Lahadi ta ce shirin tallafi ne daga Majalisar Dinkin Duniya domin tallafawa bangarori da dama su farfado daga mummunar illar annobar COVID-19, musamman mata masu dauke da cutar AIDS a Najeriya.

“Hakika annobar COVID-19 ta yi illa ga tattalin arzikin duniya musamman a nan Najeriya inda ta janyo rasa ayyuka da dama musamman ga masu karamin karfi,” inji sanarwar.

Yayin kaddamarwar, Babban Daraktan NACA, Dakta Gambo Aliyu ya ce sanadiyyar cutar, Najeriya ta gano hanyoyin matakan kariya daga kwayar cutar ta hanyar wayar da kan mutane yadda ya kamata.

Shirin dai ya kudiri aniyar tallafa wa mata musamman masu dauke da cutar AIDS wadanda annobar ta kassara harkokin tattalin arzikinsu.

Ministar harkokin mata kuma jagorar shirin, Paulin Tallen ta ce masu ruwa da tsaki da mata gajiyayyu a jihohi 15 da annobar ta fi kassarawa ne za su amfana da shirin.

Jihohin sun hada da Legas da Babban Birnin Tarayya Abuja da Kano da Sakkwato da Oyo da Edo da Ribas da Ogun da Kaduna da Borno da Gombe da Bauchi da Akwa-ibom da Delta da kuma Ebonyi.

Shugaban sashen kula da mata da kare hakkin dan Adam ta NACA, Yinka Falola-Anoemwah ta ce shirin zai samar da tallafin kudade, kayan kariya irinsu takunkumin fuska, sinadarin tsaftace hannu da sabulai ga mata, yara da matasa da annobar ta fi yi wa illa.