✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar da ke amfani da fitsari don maganin ciwon ido

Suama ta gano cewa fitsari shi ya fi kyau wajen magance matsalolin ido fiye da magungunan da aka haɗa da sinadarai.

Wata mata ’yar kasar Spain mai suna Suama Fraile ta jawo ce-ce-ku-ce bayan da ta ce ɗigon fitsarin da take ɗigawa a idonta yana warkar da ciwon ido kamar rashin gani daga nesa da kuma rashin gani sosai.

Suama Fraile ta ce fitsari a matsayin magani na maye wani magani wanda wani dan asalin Birtaniyya mai suna John W. Armstrong ya shahara a kansa, wannan nau’in magani ya gano shi a farkon Karni na 20.

Masu ba da shawarar wannan nau’i na maganin da ba a saba da shi ba suna habaka amfani da fitsarin dan Adam don magani ko kayan kwalliya, gami da tausasa fata, ko gumi har ma da shan sa.

Ko yaya, mai amfani da kafar TikTok kuma mai ba da shawara kan rashin lafiyar dan Adam, Suama ta gano cewa fitsari shi ya fi kyau wajen magance matsalolin ido fiye da magungunan da aka hada da sinadarai wadanda yawancin likitoci suka tsara?

Matar ta yi ikirarin cewa ta rika diga fitsari a idonta a kullum har sai da ta warke daga rashin gani daga nesa da kuma rashin gani sosai.

A cikin wani faifan bidiyo na TikTok da ya karade a kafofin watsa labarai, Suama Fraile ta yi bayanin cewa diga fitsari, “Yana warkarwa fiye da magungunan gargajiya,” tunda za a iya samun magani mai sinadarai da ka iya yin illa fiye da yin magani.”

Don tabbatar da ingancin fitsari a matsayin magani ga rashin hangen nesa, matar ta ba da cikakken bayani game da kwarewarta kan maganin.

“Zan gaya muku abin da na fuskanta, digon fitsari a idona da safe da daddare na warkar da ni daga ciwon rashin gani daga nesa da kuma rashin gani sosai,” in ji ta.

Ta kara da cewa, “Wannan dabi’ata ce, manta da kwayoyi, sunadarai ne, kuma hakan na shafar lafiya.”

Suama ta ce, ina amfani da fitsari a matsayin magani wanda ya yi tasiri, idan ana son ya yi aiki dole ne a rika diga ruwan fitsarin a kullum safe da yamma.

Ta kuma ce, tana amfani da fitsarin ingantacce da daddare, wanda watakila yana nufin fitsarin da bai da wani irin launi.

Kamar yadda za ku iya tunani, bidiyon da aka yada ya samu suka da yawa a shafukan Intanet, mafi yawan abin da dole ne in yarda cewa yana da tabbaci.

Abu daya ne don inganta fitsari a matsayin magani da kuma shafa fitsari a jiki da fatan samun wani nau’in fa’ida daga ciki, amma don karfafa wa mutane su sa shi a cikin idanunsu wani abu ne gaba daya.

Ni ba likita ba ce, amma wannan ga alama za a iya yin bincike! A halin yanzu babu wata shaidar kimiyya da za ta goyi bayan fa’idar amfani da fitsari don warkarwa a samu lafiya.